Mutanan wannan karni muna a cikin babbar tsaka mai wuya duba da yadda yan kananun abubuwa suke zuwa suna janye mana hankali muna sauka daga tarbiyar da addininmu ya daura mu akanta. 

Yanzu ayi duba da zuwan wannan sabuwar hanyar lalata tarbiyar mutane tiktok wacce ake yada videos na rawa da shirme harda hauka ma duk ta dauki hankalin al'ummar musulmai duk sun koma yan rawa. 

Wannan karamin abun ya dauki hankulan mutane duk sun bishi ya kuke tunanin idan dujjal yazo Allah yasa mu dace kuma ya kara shiryamu ameen.