Director Aminu saira yayi Karin bayani ko ace haske akan cigaban shirin LABARINA S3 domin kara wayar da kan mutane ko sun daina asarar data dinsu a YouTube domin sunan ganin ana saka LABARINA S3 sai su shiga domin su kalla. 

Aminu saira yace basu fara sakin cigaban wannan shiri ba wato season 3 a ko wacce kafa ta kallon zamani ba bare ma kuma basa saka shirin su a manhajar YouTube .

Ga yadda sanarwar tashi ta kasance, 

Sanarwa!!!  

Har yanzu bamu fara haska #Labarina S3 a ko wanne wuri ba, sai bayan ramadhan insha Allah, kamar yadda muka sanar a baya, akwai masu saka film din karya a YouTube da sunan #Labarina S3 bamu bane a kiyaye, mungode da soyayyarku, 1Love.