Mansurah Isah ta nemi Hadiza Gabon da Maryam Yahaya su yi karan Tanimu Akawu kan kalaman cewa matan Fim suna bin mazan banza.
Tsohuwar jarumar Kannywood, Mansurah Isah, ta mayar da martani akan kazafin da Tanimu Akawu yayi wa matan masana’antar shirya fina-finan Hausa na bin mazan banza.
Mansurah wacce ta kasance mata ga jarumi Sani danja ta bayyana cewa ya kamata Maryam Yahaya da Hadiza Gabon su maka, Tanimu Akawu a kotu dan maganin gaba.
Ta kuma yi kira ga shuwagabannin masana'antar da su shigo wannan lamari dan a kwatarwa matan masana'antar hakkinsu.
TV Hausa ta wallafa a shafinta na Facebook cewa Mansurah Isa ta bayyana cewa, matan fim jajirtattune wanda suke shige da fice dan samun na kansu, ta kara da cewa bakin ciki ne Tanimu Akawun yake dan baida shi.
Tace: “Ba yin yan matan nan bane, yin Allah ne, kuma mutum bai isa yaja da ikon Allah ba. “Kana matsayin Uba amma kana zagin yaran ka Dan kawai sunfika arziki da kudi??? Tsantsar bakin ciki kawai ba wani abu ba.”
A baya mun kawo maku cewa wani rahoto da muka samu a shafin jaridar Hausa Trust ya bayyana yadda shahararren jarumin wasan Hausan nan na masana'antar Kannywood, Alhaji Tanimu Akawu, wanda ya bayyana cewa yanzu haka ya kai kimanin shekaru goma sha takwas yana fafatawa a harkar fim.
A wata tattaunawa da aka yi dashi a wani gidan rediyo mai suna Human Right dake garin Abuja, cikin shirin dandalin fina-finai, jarumin ya bayyana cewa matan fim din suna bin mazan banza masu kudi da masu mulki.
Jarumin ya bayyana cewa motar da Hadiza Gabon ke hawa kadai za ta iya siyan motocinsa guda goma, ya kara da cewa shi EOD ce yake hawa kuma ya siye ta da kudinshi.