Dr. Isa Ali Pantami Zai Zama Shugaban Kasan Nigeria - Datti Assalafiy.
Wato tun bayan da shugaba Buhari ya tura sunan Malaminmu Ash-sheikh Dr Isah Ali Ibrahim Pantami (H) majalisa don a tantancesu saboda zai basu mukamin minista sai aka samu wasu daya cikin 'yan arewa musamman 'yan garin da Malam ya fito suna ta suka
Suna suka akan ba wai don Malam bai cancanta ya zama minista bane, suka suke saboda tsabagen hassada da banbancin ra'ayin siyasa da kuma akida na addini da manufa
Kaf cikin wadanda shugaba Buhari yace zai basu mukamin Minista banga wanda cancantarsa ta kai ga na Malam Isah Ali Pantami ba, kasancewarsa Malamin addini masani kuma kwararren 'dan boko kadai ya wadatar
Akwai wasu suna cewa wai shugaba Buhari 'dan izala ne, shiyasa ya zabo 'dan uwansa 'dan izala zai bashi mukamin Minista, to da zamu tambayesu Rotimi Ameachi shima 'dan izala ne??
Don haka duk inda aka kai aka koma za'a ga cewa hassada ce kawai take damun wasu daga cikin 'yan arewa.
Bayan haka, mahassadan sun fara rubutu cewa zasu zuba ido su gani Malam zai yi wa sandar 'yan majalisa (mace) sujjada kamar yadda akeyi a al'ada ko kuwa ba zaiyi ba saboda su samu abinda zasu soke shi, mahassada ku zuba ido ku kalli abinda zai faru idan anzo tantance Malam, Insha Allahu 'yan kishin islama zasu kafa tarihi
Kuma da irin wannan bakar hassada na rashin dalili babu inda za'a je, haka za'a dawwama cikin matsaloli a wannan yanki namu na arewa har sai mun gyara
Tabbas masu hikimar magana sunyi daidai da sukace rashin sani yafi dare duhu, da kunsan kyakkyawar manufa dake zuciyar Malam Isah Ali Pantami game da makomar addininmu da yankin mu na arewa, da taimakon da yayi a mukamin DG NITDA da ya rike da ba'a samu wanda zai soke shi ba balle har ya kalubalanci cancantarsa
Kuma indai muna raye watan watarana Malam Isah Ali Ibrahim Pantami sai ya zama shugaban Kasar mu Nigeria INSHA ALLAHU.