Saratu Gidado Na Nema Wa Tsohuwar Jaruma Bilkin R.K. Agajin Gaggawa.

Post by <> samaila umar lameedo

Ga abin da fitacciyar jaruma Hajiya Saratu Gidado (Daso) ta rubuta:
"Wannan baiwar Allah da mu ka yi hotuna da ita sunan ta BILKIN R.K.
Tsohuwar jarumar films din Hausa ce. Ta yi zamani da su Hindatu Bashir da marigayiya Biba. Ta bada gudunmawa sosai don ci-gaban films.
Ta na fama da ciwon sabara da ciwon kirji da "low blood". Ta rame sosai. Ba ta da mai taimako sai Allah. Ga ta marainiya kuma ba ta da d'a, ga shekaru sun hau mata.
Wanda Allah ya nufa ya na iya taimaka mata da kudin magani ko kayan abinci.
Ga lambar wayar ta nan 08036144627 mai so ya yi magana da ita.
Ko kuma ta bank details di na:
Saratu Gidado
Zenith Bank
1003795458
Ita ta ba ni izini in sanar wa jama'a ko za a dace.
Allah ya bada ikon taimakawa."👏
Sources:Fim magazine