Mun cancanta ka Bamu kujerar minista daya |yan hausa film ga Buhari.

Masu ruwa da tsaki a masana'antar Kannywood a ranar Litinin sun yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari ya basu kujerar minista daya.
Daya daga cikin shugabannin masana'antar kuma diraktan Abnur Entertainment, AbdurRahman Muhammad, wanda akafi sani da Abdul amart, ya bayyana cewa suna mika wannan bukata ne saboda rawar da masana'antar ta taka wajen ganin shugaba Buhari ya samu nasara a zaben 2015 da 2019.
Mista Amart, wanda yayi magana da Daily Trust a ranar Litinin, ya ce mawakan Kannywood, jaruman fim, da sauransu sun yiwa Buhri yakin neman zabe a dukkan sassan arewacin Najeriya.
A cewarsa, wannan abu da sukayi ya kamata asaka musu da kujerar minista daya.
Yace: "Mun taka rawar gani a zaben shugaba Buhari, mun jawo hankulan masu kallonmu, kuma bisa ga bincikenmu, mun sanya mutane da yawa zaben Buhari a 2015 da 2019."
"Mun san ya ci zabe a 2015 da 2019 amma mun taka rawar gani wajen miliyoyin kuri'ub da ya samu, saboda mun yi masa wakoki masu kyau, kun yi masa yakin neman zabe gida-gida."
Ya kara da cewa duk da rawar da suka taka a 2015, babu abinda suka samu daga gwamnatin Buhari. Saboda haka a wannan karon, suna sauraron Buhari ya basu mukami.