Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa'ad Muhammad Yayi Sanarwa.

Labarin da muke kawo muku kai tsaye daga fadar mai alfarma sarkin Musulmi, Sultan Abubaakar Sa'ad na nuna cewa an ga sabuwar jaririyar watar Shawwal, a yau Litinin 29 ga watan Ramadan wanda yayi daidai da 3 ga watan Yuni, 2019.
Sarkin Musulmi ya sanar da cewa gobe, ranar Talata ce 1 ga watan Shawwal kuma Sallar Idi
Yace: Bisa ga shari'ar Musulmi, muna masu sanar muku da cewa a yau Litinin 3 ga watan Yuni 2019 wanda yayi daidai da 29 ga watan Ramadan 1440, ne karshen watan Ramadana na shekarar 1440AH."
"Mun samu rahotannin tabbacin ganin wata daga shugabannin adinin Musulunci daga gari daban-daban.. Mai martaba Shehun Borno, Sarkin Gwandu, Sarkin Jema'a, Sarkin Damaturu, da wasu sa sassan jihar sokoto
Bisa da haka, gobe Talata 4 ga watan Yuni, 2019 ta zama 1 ga watan Shawwal 1440AH kuma ranar Sallah. Muna rokon Allah ya karba ibadun da mukayi a cikin watar Ramadan."
Source: Legit