Rabi,u sheriff usman baba Allah yayi masa rasuwa a yau hudu ga watan ramadan.

Da sanyin safiyar yau Alhamis hudu 4 ga watan Ramadan, wanda yayi daidai da tara 9 ga watan Mayu na wannan shekarar, Allah yayiwa fitaccen Sha'irin nan wato Sheriff Rabi'u Usman Baba rasuwa.
Majiyar mu ta ruwaito cewa za'a gudanar da jana'izar fittacen Sha'irin kamar yada addinin Muslunci yatanadar a gidansa dake kofa ta biyu (second gate) dake unguwar Janbulo a cikin birnin Kano.
Rabi'u Usman Baba ya shahara wajen rera wakokin yabo ga fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S.a.w) da iyalansa inda har yaciri tutar zama shugaban kungiyar Shu'ara'ul Islam ta Najeriya baki daya kafin rayuwarsa.
Daruruwan jama'a na cigaba da bayyana alhininsu game da mutuwar fitaccen Sha'irin tare da jimamin rashin sa, duba yadda wakokin sa sukayi tasiri a tsakanin mabiya darikar Tijjaniyya da kuma Kadiriyya.

Fatan Allah yagafarta masa