Kotu ta bada dama kwamishinan yan sanda da ya kamo hadiza Gabon.

A yaune Alhamis mai shari'a muntari dandago na kotun magistrate court 15 dake zamanta nomansland ya bawa komishinan yan sanda na jihar kano umarni ya kamo shahararriyar jarumar wasan Hausa hadiza Gabon sabida taki amsa kiran kotun.
Mustapha na buriska shine ya shigar da karar jarumar yana zarginta da cewa tanayi masa barazana da rayuwa ya yanke shawarar maka ta kai tsaye zuwa kotu saboda saboda yana tsoron idan ya kaiwa hukumar yan sanda bazata tuhme ta ba kasancewar yadda jarumar takeda mu'amala da wasu daga cikin jami'an yan sanda da kuma manyan yan siyasa dama masu kudi a fadin kasar nan.
Mai shari'ar ya bada umarnin hakan saboda bijirewa gayyatar da kotu ta 1 tayi mata kuma ya kara da cewa idan kwaminshinan yan sanda ya kamata ya tabbatar an binciketa akan lainfin da mai karar ya shigar kafin a damkata ga hannun kotun suma suyi nasu hukuncin.