Amina Amal ta maka Hadiza Gabon Kotu saboda dukan data sa aka yi mata da cin zarafi. 

Amina Amal, jaruma a masana’antar Kannywood ta mika jaruma Hadiza Gabon gaban kuliya domin neman hakkinta.
Amina Amal ta fitar da takarda dauke da saka hannunta tare da jerin sunayen Lauyoyin da zasu kareta a gaban kuliya manta sabo
Takarda daga Kamfanin Amina Amal
“Ni Amina Muhammad Amal, nayi wannan rubutu ne domin shirye-shiryen da nake na daukar wadannan Lauyoyin don yin aiki a madadin kaina bisa wulakanci da cin zarafin da wata Hadiza Gabon tayi min.”