[post by samaila umar lameedo]

Zan kammala dukkanin ayyukan da PDP ta watsar a Kudu maso Gabas - Buhari

Da sanadin shafin jaridar The Punch mun samu rahoton cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sha alwashin kammala dukkanin wasu ayyuka da jam'iyyar adawa ta PDP ta watsar a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Mun samu cewa, shugaban kasa Muhammadu ya lashi takobi tare da kudirtar kammala duk wasu ayyuka da babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta watsar a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da manema labarai cikin karamar hukumar Ihitte da kuma Uboma ta jihar Imo da ke Kudu maso Gabshin kasar nan a ranar Alhamis din da ta gabata.
Zan kammala dukkanin ayyukan da PDP ta watsar a Kudu maso Gabas - Buhari
Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaba Buhari ya yi wannan furuci yayin halartar bikin kaddamar katafaren aiki na kula da hana zaizayar kasa, inda ya ce yankin Kudu maso Gabashin Najeriya za su ci moriya tareda kwankwadar romon na jin dadi muddin ya yin nasara a zaben watan gobe.
Shugaban kasar wanda Ministansa na Kimiyya da Fasaha ya wakilta, Ogbennaya Onu, ya bayyana cewa, ba bu gaskiya dangane da ikirarin 'yan adawa kan cewa shugaba Buhari ba ya yiwa yankin Kudu maso Gabashin kasar nan adalci.
A cewar Onu, gwamnatin shugaba Buhari ta sha alwashin dukufa gami da fafutika wajen tabbatar da karasa dukkanin wasu ayyuka da jam'iyyar adawa ta PDP ta watsar a yankunan Kudu maso Gabashin Najeriya.
Ya kara da cewa, wannan muhimmin aiki na kula da zaizayar kasa zai taimaka kwarai da aniyya wajen inganta ci gaban gine-gine, tare da bayar da kariya da tsare rayuka da dukiyoyin al'umma a yankin.