[post by samaila umar lameedo]

'Yan sanda sun kama Sanata Dino Melaye
LABARAI DAGA 24BLOG
Dan majalisar dattawan Najeriya, Sanata Dino Melaye, ya mika kansa ga rundunar 'yan sandan kasar.
Ya mika kan nasa ne bayan an girke jami'an 'yan sanda masu dimbin yawa kusan mako daya suna yi wa gidansa kawanya.
'Yan sandan suna zargin dan majalisar ne da yunkurin kashe wani jami'in dan sanda mai suna Danjuma Saliu a ranar 19 ga watan Yulin 2018.
Sai dai ya musanta zargin.
Wakilin BBC da ya je gidan Sanata Dino Melaye lokacin da aka tafi da shi, ya ce 'yan sandan sun tafi da shi ofishin rundunar 'yan sandan da ke yaki da 'yan fashi da makami, SARS.
'Yan sanda sun girke na'urar toshe sadarwa a gidan Dino Melaye
SARS dai ta yi kaurin suna wurin kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba.
Da ma Sanata Dino Melaye ya sha cewa ya ki mika kansa ga rundunar 'yan sandan ce saboda zargin za su yi masa allurar mutuwa, ko da yake 'yan sandan sun musata zargin.
Ranar Laraba ne rundunar 'yan sandan ta girke na'urar toshe sadarwa a kofar gidan Sanata Dino Melaye.
Hakan baya rasa nasaba da wani sakon Twitter da ya wallafa a safiyar Larabar wanda yake nuni da cewa 'yan sandan suna kawo kayayyaki domin su fasa kofofin shiga gidansa.