Yadda Buhari yawa 'yan jiharshi ta Katsina sata<>Atiku

Dan takarar jam'iyyar PDP a zaben shugaban kasa me zuwa, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana yanda yace jam'iyyar APC da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke kokarin sacewa 'yan Najeriya kuri'unsu.
Atiku ya bayyana hakane a jihar Ekiti inda yaje yakin neman zabe ya kuma tabbatar wa da jama'ar jihar cewa bazai manta dasu kamar yanda Buhari ya manta da su ba.
Atiku yace abin kunyane ga shugaba Buhari ace har mutanen jiharshi be barsu ba saida ya musu sata.
Atiku yace, mutanen arziki 'yan jihar Ekiti ku sani cewa APC ta sace muku ayyukan da kuke dasu, kuma tana nan tana shirin sace muku kuri'unku kamar yanda tayi a jihohin Osun, Bauchi, Ogun da Ekiti har dama jihar Katsina inda suka fito, bansan me yasa har mutanen su basu bari ba sai da suka musu sata.
Ya kara da cewa zasu gyara tituna da kuma dawo da martabar ilimi da samar da ayyuka, ya kara da cewa zasu baiwa mata kashi 30 cikin dari na mukaman da zasu nada da kuma matasa za'a basu kashi 40, gaba daya kashi 70 kenan.
Yace APC bata san yanda ake samar da ayyukan yi ba amma su sun sani, sun kuma ayi a baya kuma zasu sake yi, kamar yanda Dailypost ta tuwaito.