[post by samaila umar lameedo]

Wanne hali Dino Melaye ke ciki?

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce dan majalisar dattawan kasar, Sanata Dino Melaye, yana cikin yanayi mai kyau bayan ya gamu da larura lokacin da jami'anta suka yi awon-gaba da shi.
A ranar Juma'a ne Sanata Melaye ya mika kansa ga rundunar 'yan sandan kasar bayan ta girke jami'anta masu dimbin yawa kusan mako daya suna yi wa gidansa kawanya.
Sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan, Jimoh Moshood, aike wa manema labarai ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan dan majalisar kuma da zarar an kammala za a mika shi gaban kotu.
'Yan sandan suna zargin dan majalisar ne da yunkurin kashe wani jami'in dan sanda mai suna Danjuma Saliu a ranar 19 ga watan Yulin 2018.
Sai dai ya musanta zargin.
Dino Melaye ya mika kansa ga 'yan sanda
'Yan sanda sun yi nasara kan Dino Malaye
Mr Moshood ya ce an girke 'yan sanda a kofar gidan Sanata Melaye ne saboda ya ki amsa gayyatar da suka yi masa domin ya yi bayani kan zargin yunkurin kisan kan da ake yi masa.
Da ma Sanata Dino Melaye ya sha cewa ya ki mika kansa ga rundunar 'yan sandan ce saboda zargin za su yi masa allurar mutuwa, ko da yake 'yan sandan sun musata zargin.
Ranar Laraba ne rundunar 'yan sandan ta girke na'urar toshe sadarwa a kofar gidan Sanata Dino Melaye.
Hakan baya rasa nasaba da wani sakon Twitter da ya wallafa a safiyar Larabar wanda yake nuni da cewa 'yan sandan suna kawo kayayyaki domin su fasa kofofin shiga gidansa.