[post by samaila umar lameedo]

Sojojin Najeriya 'sun fatattaki' Boko Haram daga Baga

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta fatattaki mayakan kungiyar Boko Haram da suka kai wa dakarun kasashen yankin tafkin Chadi mai shedkwata a Baga hari a 'yan makwannin da suka gabata.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce wasu dakarun kundumbala na sojojin Najeriya sun kashe 'yan kungiyar Boko Haram bangare da ya yi mubaya'a ga kungiyar IS mai da'awar kafa daular musulunci da dama, a harin.
Mazauna yankin na Baga dai sun ce mayakan na Boko Haram da suka yi mubaya'a ga kungiyar da ke da'awar kafa daular musulunci a yammacin Afirk ke iko da garin na Baga.
Sai dai rundunar sojan Najeriya ta musanta cewa garin yana hannun Boko Haram.
Rundunar Sojin Najeriya za ta kwashe mutane daga Baga
Sojoji sun murkushe hare-haren Boko Haram a Baga
Sanarwar da Janar da daraktan yada labaran rundunar Janaral Sani Kukasheka Usman ya fitar ta ce, sojojin na musamman sun kuma kakkabe 'yan Boko Haram daga wasu garuruwa da ke kan hanya, kamar Kukawa da Gudumbali da Kuros Kauwa, har ma ta samu nasarar kwato wasu makamai.
Sanarwar na nuna cewa a yanzu dakarun kasar ne ke da iko da Garin Baga, domin kuwa tuni dakarun na musamman suka hade da sojojin da ke Baga, wadanda suka fatattaki 'yan Boko Haram.
Sai dai sanarwar ta ce an kashe sojoji biyu yayin fafatawar, sannan wasu biyar kuma sun jikkata.
Gagarumin aikin na hadin gwiwa ne tsakanin sojojin kasa da na sama da kuma na ruwa.