Rabiu Biyora ya bayyana abinda Atiku ya gayamai

Tauraron me goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari a Facebook da ya koma goyon bayan Atiku Abubakar, Rabiu Biyora ya bayyana abinda Atikun ya gayamai.
Ina son kasancewa shugaban Nigeria ne, don samar da kyakkyawar rayuwa ga al'ummar kasa, inga arziki ya yawaita a dukkan gidaje, yan Nigeria su amfana da arzikin kasarsu ta yadda abunci da kayan masarufi zasu dena wahalar dasu.
Zanyi amfani da kwarewata a fannin tattalin arziki, wajen janyo manya manyan Kamfanonin duniya zuwa Nigeria, musammam yankin Arewa da masana'antu suka durkushe..
Bani da burin daya wuce inga al'umma cikin kwanciyar hankali da wadata tunda Allah ya basu arzikin da zasu kasance cikin wadatar....
Rabiu ina tabbatar maka da cewa matasa ne zasu kasance a gaba idan na zama shugaban Nigeria, domin sune ya kamata su jagoranci kasarsu kuma suke dauke da sabbin dabarun da zasu temaka wajen kawowa Nigeria babban cigaba a dukkan bangarori.