[post by samaila umar lameedo]

PDP ta fara karfi a wata jihar arewa yayinda yan APC da PDM 4,500 suka koma jam’iyyar

- Jam’iyyar PDP ta yi babban kamu a jihar Niger inda ta samu sabbin mambobi 4,500
- Mutum 1,500 sun sauya sheka ne daga jam’iyyar PDM yayinda 3,000 kuma suka kasace yan APC
Mambobin jam’iyyar People Democratic Party (PDP) a jihar Niger a ranar Juma’a, 4 ga watan Janairu sun yi babban kamu gabannin shiga watan zabe, inda suka tarbi mambobin jam’iyyar People Democratic Movement (PDM) daga karamar hukumar Chanchaga da ke jihar.
Dukkanin surar jam’iyyar a yankuna 11 na Chancaga ya rushe zuwa PDP dauke da mambobi 1,500.
Masu sauya shekar sun samu jagorancin shugaban jam’iyyar na karamar hukumar, Hon. Suleiman Alhassan inda suka samu tarba daga shugaban PDP na karamar hukumar, Hon. Jamilu Saidu a wani biki da aka shirya a garin Minna a ranar Juma’a.
2019: PDP ta fara karfi a wata jihar arewa yayinda yan APC da PDM 4,500 suka koma jam’iyyar
Hakan na zuwa ne kasa da mako guda bayan shugaban PDP a jihar, Alhaji Tanko Beji ya tarbi mambonbin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) 3,000 daga karamar hukumar Edati da ke jihar.
Da yake Magana a madadin masu sauya sheka, shugaban PDM a karamar hukumar Chanchaga, Hon. Suleiman Saidu, yace sun yanke shwarar haewa da PDP ne saboda sunyarda cewa jam’iyyar ce kadai ke da ikon hade dukkanin yan Najeriya sannan ta kawo ci gaba da kuma dinke barakar kabilanci da sauransu.