[post by samaila umar lameedo]

Ole Gunnar Solskjaer: 'Ba na son barin Man Utd'

Kocin riko na Manchester United Ole Gunnar Solskjaer ya ce ba ya son sauka daga aikinsa a karshen kakar wasa mai zuwa.
An nada shi a matsayin koci na rikon kwarya bayan da kungiyar ta kori Jose Mourinho a watan Disemba.
Nasarar da kungiyar ta samu tsakaninta da Newcastle a ranar Laraba, inda ta yi nasara da ci 2-0, ya sa sabon kocin ya zama koci na biyu a tarihin kungiyar da ya lashe wasanni hudu a jere kamar yadda Sir Matt Busby ya yi a shekarar 1946.
Solskjaer ya fara ci wa Manchester United kwallaye biyar
Solskjaer 'ya zama sabon kocin' Manchester United
Solskjaer ya zama kocin Cardiff City
Da aka tambaye shi ko zai bar kungiyar a watan Mayu, sai ya bayyana cewa "baya so ya tafi."
Solskjaer dai ya samu wannan mukamin ne bayan ya samu izini daga kungiyar kwallon kafa ta Molde duk da cewa kungiyar ta bayar da shi aro ne ga Manchester, inda kungiyar ta bayyana cewa tana sa ran zai dawo a matsayin kocinta.
Idan aka kwatanta shi da Matt Busby wanda ya ci gasar lig biyar tsakanin shekarun 1945 zuwa 1969 da kuma 1970 zuwa 1971, Solskjaer ya ce: ''Wannan abin tarihi ne, amma ba wani abin da nake tunani ba ne."
"Ina tunanin wasan mu na gaba ne, saboda idan na ci wasanni hudu, toh lallai zan iya cin hudu na gaba a wannan kungiyar, wannan kalubale ne a gare mu, kuma dama mun saba fuskantar irin wannan kalubalen."