Kungiyar Izala ta bukaci mabiyanta su zabi Buhari a 2019

Kungiyar Izala daya daga cikin manyan kungiyoyin addinin Islama a Najeriya ta ce shugaba Buhari take goyon baya a zaben 2019.
Shugaban kungiyar na kasa Shiekh Abdullahi Bala Lau wanda ya tabbatar wa da BBC da matakin, ya ce sun yanke shawarar ne bayan wani taro na kasa da suka gudanar.
Ya ce sun lura yadda ake fuskantar lokacin zabe mawuyaci, ya kamata a yi saitin al'ummar musulmi kan abin da ya kamata.
Bala Lau wanda a baya ya ce ya tunatar da Buhari kan halin da talakawa suke ciki
a wata ganawa da suka yi a fadarsa, ya ce "sun janyo hankalin al'umma cewa a lokacin zabe mai zuwa a lura da wannan shugaba mai adalci kan irin kokarin da ya soma a sake ba shi goyon baya don ya ci gaba."
"Allah ya kawo saukin ringigimu da tashin bama-bamai dalilin zuwan shugaba Buhari, illa dan abin da ya rage na fitintinun Allah zai kawo saukinsu."
"Don haka akwai bukatar a sake ba shi goyon baya saboda irin kudirinsa na kulawa da tausayi da tabbatar da zaman lafiya," in ji shi.
Akwai dai wani bangare na Izala da ke adawa da sake zaben Buhari a zaben 2019, inda ake ganin hakan ya raba kan 'ya'yan kungiyar.
Bai kamata a sake zaben Buhari ba - Dattawan Arewa
Na fada wa Buhari halin da talakawa suke ciki - Sheikh Bala Lau
Da aka tambayi Bala Lau, shin ko Izala ta koma kungiyar siyasa ne, sai ya ce "Izala kungiya ce ta addini da ke wa'azi da shiryar da al'umma."
"Ba kungiyar siyasa ba ce sai dai tana la'akari wajen sanya 'ya'yanta kan abin da ya kamata," in ji shi.
Ya kuma ce, duk da Izala ba kungiyar siyasa ba ce amma kungiya ce mai wa'azi da ke cewa kada a yi kaza don Allah ba ya so.
An tambaye Bala Lau, ko uwar kungiyar ta yi la'akari da ra'ayoyin mambobinta a siyasance kan sauran 'yan takarar shugaban kasa, sai ya ce "ai abin da suka yi bai saba wa shari'a ba."
"Dole mu auna mu ga cewa wane ne idan ya shugabanci al'umma zai zamanto ya kare addininsu da jininsu da dukiya da hankali da nasabarsu."
"Mun samu shugaba jarumi mai amana kuma mai adalci, to dole mu auna mu ga wa ya cancanta kuma ba laifi ba ne idan bai saba wa shari'a ba."
Ya ce su ba 'yan siyasa ba ne kuma ba 'yan jam'iyyar APC ba ne.
Sai dai ya ce ba su takaitawa mabiyan kungiyar ba cewa dole su yi jam'iyya daya tak wajen zaben sauran 'yan takarar da suka cancanta na sauran jam'iyyu da ke neman sauran mukamai.
"Amma wajen shugabancin Najeriya kungiyar Izala ta gamsu da salon mulkin Buhari kuma abin da yake yi daidai ne don haka muke goyon bayan ya sake samun nasara a karo na biyu.
Ya ce reshen kungiyar a jihohi 34 na Najeriya suka amince da matakin kungiyar na marawa Buhari baya a zaben 2019.
"Jihohi 34 daga cikin 36 da suka zo mun tambaye su ga abin da muke su, kuma suka ce sun amince sun yadda da muka yi haka."