[post by samaila umar lameedo]

Karanta amsar da Rahama sadau ta baiwa wani da ya tambayeta - Naji ance kin koma Kirista

baya anyi rade-radin cewa, tauraruwar fina-finan Hausa da turanci, Rahama Sadau wai ta koma Kirista dalilin korar da aka mata daga masana'antar fim din Hausa da kuma zuwa kasar Amurka da tayi, tuni dai wancan labari ya wuce dan kuwa jarumar ta karyatashi tun a wancan lokacin.
Wani bawan Allah ya yiwa Rahama tambayar cewa, naji jita-jitar cewa wai kin zama kirista amma ban yarda ba, gaskiyane ko kuwa a'a?.
Rahama ta mayarmai da amsar cewa, naji cewa yanzu kai ba mutum bane da gaskene?