Duk Wanda Ya Ke Kukan Yunwa Da Talauci A Gwamnatin Buhari A Koshe Ya Ke<>Manazarta

Matashi Aliyu Dr. Habibu Gwarzo tare da Dattijo Habibu Muhammadu Sani manazarta akan ayyukan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wadanda suka kirkiro shirin wayar da kan al'umma kyawawan manufofin wannan gwamnati mai suna "DON TUWON GOBE" sun bayyana Buhari a matsayin Shugaban Kasa mafi yi wa Nijeriya aiki.
"Idan aka dauki farfado da tattalin arzikin kasa, a baya gwamnatin Jonathan ta samu kudin da ba wata gwamnati a Najeriya da ta taba samun irinsa. Maimakon su yi amfani da wannan damar su gina kasa, amma aka rika kwasa ana azurta wasu kasashen ana talauta Najeriya. Daidai da tsinken sakace sai an kwashi Dala an sayo daga wata kasar. A baya shinkafa kadai akan sayo shinkafa ta Dala Miliyan Biyar a kullum, amma a yanzu ba a sayo ta sama da Dala 500 kuma ana hasashen nan gaba sai dai mu sayarwa da wasu shinkafa.
Da zuwan Buhari ya yi amfani da wani tsari na zubawa da kashewa, wanda idan tattalin arziki ya zama kwasa ya fi yawa akwai matsala sai dai zubawa ya fi yawa. Sannan Kudaden aka yi musu asusun banki daya wanda sai da aka rufe na bogi kusan 25,000 da kudade kusan Tiriliyan biyar.
Sannan batun lantarki an samar da megawas 7,000 sannan idan aka gama aikin Mambila zai samar da Megawas 3050. Ga harkar Noma ga harkar tallafi ga titunan Jirgin kasa da manyan tituna saboda saukaka sufuri domin bunkasa Kasuwanci. An fito da tsarin tallafawa 'yan fim da mawaka gami da harkar bayar da bashi domin taimakawa kananan 'yan kasuwa. Duk mutumin da ya fito yana kukan talauci da yunwa a koshe ya ke, domin ana cin Abinci sau uku a gidansa kuma shi bai taimaki kowa ba.
Gwamnati ta fito da harkar tallafawa mutane da jari idan wannan abu ya dore, mutane za su zama kananan Dangote su daina laruwa da gwamnati ta ba su aiki.
Rariya.