[post by samaila umar lameedo]

Da addu’o’inku zan yi nasara akan PDP, YPP, ACPN da sauransu - Buhari

- Buhari ya nemi taimakon cocin Cherubim and Seraphim Unification Church of Nigeria da addu’a domin ya samu ya yi nasara a zaben 2019
- Shugaban kasar ya bukaci hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban cocin a fadar shugaban kasa da ke Abuja
- Shugaban tawagar, Prophet (Dr) Solomon Adegboyega Alao, ya fada ma shugaba Buhari da ya mayar da hankali ga aikin alkhairin da yake yi musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a ranar Juma’a, 4 ga watan Janair ya bukaci taimakon cocin Cherubim and Seraphim Unification Church of Nigeria da addu’a domin ya samu ya yi nasara a zaben 2019 mai zuwa.
Buhari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin shugaban cocin a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Da addu’o’inku zan yi nasara akan PDP, YPP, ACPN da sauransu - Buhari
“Na yi matukar farin ciki da ziyarar. Allah zai amsa addu’o’inmu. Da addu’o’inku, za mu shiga filin daga, sannan mu yi nasara. Mun gode da kudirori da addu’o’inku masu kyau. Wannan shine abunda muke bukata daga cibiyoyi masu yi wa Allah aiki, ” Inji shugaban kasa.
Shugaba Buhari yace yayi farin ciki da yabawa kyawawan ayyukan gwamnatinsa da cocin suka yi a fannin ababen more rayuwa, yaki da rashawa da kuma tsaro, inda ya katra da cewa “hakan zai karfafa mana gwiwar sake zage damtse. Ba mu da wata kasar bayan Najerya, kuma ya zama dole mu yi iya bakin kokarinmu don ganin ta inganta. Mun gode da kuka gane manufarmu.”
Shugaban tawagar, Prophet (Dr) Solomon Adegboyega Alao, ya fada ma shugaba Buhari da ya mayar da hankali ga aikin alkhairin da yake yi musamman wajen yaki da cin hanci da rashawa inda ya kara da cewa
“Mun san cewa cin hanci da rashawa wanda ke kashe Najeriya na iya yunkurin rama yaki amma ba zai cimma nasara ba saboda mafi akasarin yan najeriya na tare da kai."
Bakin sun bukaci shugaban kasar da yayi amfani da karfin kujerarsa wajen ganin an saki Leah Sharibu wacce ke a hannun yan ta’addan Boko Haram saboda ta ki barin addininta, sannan kuma cewa ya tabbatar hukumar abe mai zaman kanta tayi zabe na gaskiya.