Buhari sai ya mulki kasarnan a karo na ukku daga 2023 har zuwa 2027<>Ibrahim Maishunku.

Tauraron fina-finan Hausa, Ibrahim Maishunku ya bayyana cewa idan Allah ya yarda shugaban kasa, Muhammadu Buhari sai yayi mulki a karo na uku a kasarnan, Maisunku ya bayyana haka a dandalinshi na sada zumunta.
Maishunku ya mayar da martanine akan masu zaginshi saboda soyayyar da yake nunawa shugaban kasa, Muhammadu Buhari inda yace, bana son bawa kowa amsa game da zagi na cin mutunci da kirana da sunaye, har wani yace min wai Kafiri.
Amma idan na tuna cewa idan mutum ya tsaya jifar duk karen dake mishi haushi bazai kai ga inda yake son kaiwa ba. Wannan ba zai hanani kiran mutane zuwa mataki na gababa, kuma yunkurin mulki na uku da Obasanjo be yi nasara akai ba zai yi nasara akan shugaba Buhari ya kaimu mataki na sama daga shekarar 2023 zuwa 2027 watau 8+4, fatan mu Allah ya bashi lafiya.