Ban bar matana a dakin kurya dana dafa abinci ba_Atiku yawa Shugaba Buhari shagube

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya yiwa shugaban kasa, Muhammadu Buhari shagube bisa kalmarnan da aka sanshi da ita ta dakin kurya, wadda a wata hira da aka yi dashi yace matarshi aikinta yana dakin dafa abinci dana kurya to shi Atiku yace be bar matanshi a dakin kurya kawai ba.
Atikun ya bayyana hakane a wajan wani taro da yayi da mata a Abuja, inda ya bayyana musu cewa zai basu fiye da kashi 35 na wakilci a gwamnatinshi idan yaci zabe, kamar yanda Independent ta ruwaito.
Atiku yace a tarihin siyasarshi ya lura da cewa matane suka fi bayar da gudummuwa fiye da maza wajan zabe akai-akai dan haka suka cancanci a basu wakilci me karfi a gwamnati, Atiku yace da mata da matasa zai basu wakilci me karfi a gwamnatinshi dan ya shiryasu karbar ragamar mulkin kasarnan nan gaba.
Ya kara da cewa shi bai bar matanshi a dakin kurya da na dafa abinci ba kawai, kamar yanda ake gani gasunan ya fito dasu.
Itama matarshi ta farko, Titi Abubakar ta bayyana cewa, mijinsu be musu kulle ba, be barsu a dakin kurya dana dafa abinci ba kadai, ya barsu su shiga ko ina su yi kasuwancinsu. Ta yi kira ga matan da su zabi Atiku dan zai samar da ikin yi.