Babbar magana<>Likita yayi wa maras lafiya ciki

A asibitin yankin Arizona kasar Amurka,an yi wata maras lafiya wacce ta share shekaru 10 a cikin doguwar ciki.
A cewar kafafan yada labaran kasar Amurka, tuni 'yan sandan garin Phoenix sun fara zurfafa bincike a asibitin Hacienda HealthCare inda abin kunyar ya faru,da nufin gano wanda ya yi wa matar fyade.
A tsawon shekaru 10 an ci gaba da ciyar da matar wacce ta tsuduma doguwar suma bayan wata nutsewa da ta yi a ruwa, ta hanyar amfani da na'ura.Amma kwastam sai a ranar 29 ga watan Disamban shekarar bara ta haifu bayan yi ma ta fyade da ake zargin likitan da ake jinyar ta.
Ma'aikatan asibitin sun tabbatar da cewa ba su da wata masaniya game da cikin matar har sai ranar ta haifu inji labaran da jaridun yankin Arizona suka rawaito.An sanar da cewa uwa da jinjirinta na lafiya kalau.
Kakakin asibitin Hacienda HealthCare,Nancy Salmon kuma cewa ya yi,ana ci gaba da gudanar da bincike shi yasa ba zai kara furta wata kalma game da wannan lamarin.
TRThausa.