[post by samaila umar lameedo]

ASUU ta amince za ta shiga a dama da ita a zabe

Kungiyar malaman jami’a (ASUU) ta amince da shiga a dama da ita a zabe mai zuwa.
An shiga yarjejeniyar ne bayan wani ganawa tsakanin hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da jami’an kungiyar a Abuja.
Mahmood Yakubu, shugaban INEC, a ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu ya tayar da wani batun cewa daga jami’o’i ne abokan aikinsu da dama suke.
Ci gaban na zuwa ne bayan ASUU reshen jami’ar Ibadan sun fada ma INEC cewa kada ta dogara da dalibai da malamai a zabe mai zuwa.