[post by samaila umar lameedo]

An samu raguwar kwararar 'yan cirani a Turai

Wani bincike da aka gudanar ya gano an samu raguwa matuka ta kwararar 'yan cirani da ke son shiga kasashen turai.
Binciken da hukumar Blocs borders agency da ke hana 'yan cirani tafiyar kasada, ya cewa cikin shekaru biyar da suka gabata an samu raguwar mutanen. 'Yan cirano 150,000 ne aka yi wa rijista a cibiyar da ake ajiye su a shekarar 2013 kuma tun daga lokacin adadin ke kara raguwa.
Hukumar bloc borders agency atakan da kasar Italiya ta dauka na haramtawa jiragen ruwan kungiyoyin agaji gudanar da aikin ceto a tekun Bahar Rum na daga cikin dalilan da suka janyo wannan raguwa.
Sai dai bloc borders agency ta ce kasar Sifaniya ita ce a sahun gaba na kwararar 'yan ciranin a dan tsakanin nan.
Wata kididdiga kuma ta nuna a shekarar da ta gabata an samu raguwa da kashi 93 cikin dari idan aka kwatanta da abin da aka gani a shekarar 2015 a lokacin da matsalar 'yan cirani ta addabi kasashen turai.
Harwayau, kididdigar da aka fitar ta shekarar 2017 ta nuna yadda aka samu raguwar 'yan ciranin da ke nikar gari daga wasu kasashen Afirka zuwa kasar Italiya da nufin samun ingantacciyar rayuwa ko gujewa yaki, da rikicin kabilanci da na siyasa da bakin talauci.
A wannan shekarar an samu raguwa da kashi 80 cikin 100, ya yin da aka yi rijistar 'yan cirani 23,000.
Haka kuma, cikin shekara guda an samu wata raguwar ta 'yan ciranin da ke bi ta kasar Libya zuwa tsuburin Lamfadusa na Italiya da kashi 87 cikin 100. Ya yin da a iya cewa kasar Algeria kuma ta samu sassaucin hakan fiye da makofciyarta.
Sai dai masu tafiyar kasada ba bisa ka'ida ba daga kasar Morocco sun addabi Sifaniya inda suka rubanya adadin shekarar 2017 zuwa da 18.