[post by samaila umar lameedo]

An far ma Faston da ya yi busharar mutuwar babban limami

LABARAI DAGA 24BLOG
Wasu matasa musulmi a Ghana sun kai wa wata coci a babban birnin kasar, Accra, hari bayan da Faston coci ya bayyana cewa an yi masa bushara cewa babban limamin kasar Ghana zai mutu a 2019.
Sun lalata kujeru da tagogi a cocin ta Rabaren Isaac Owisu-Bempah.
Babban limanin kasar Nuhu Sharabutu, wanda Faston ya ce zai mutu, ya yi Allah wadai da harin.
Fasto ya nemi afuwa bisa taba maman mawakiya Ariana Grande
Ana zargin fasto da yi wa wata mata fyade
Kada ya cinye wani fasto yana wankan tsarki a kogi
A wa'azin Rabaren Isaac na ranar 31 ga watan Disamba ne ya bayyana busharar abubuwa 18 da za su faru a 2019, daga ciki hadda mutuwar dayan cikin wadannan biyu, ko babban limamin kasar, Nuhu Sharabutu, ko mataimakin shugaban kasar Ghana, Mahamudu Bawumia.
Wasu matasa musulmi sun nemi da ya ba da hakuri a kan furucin nasa amma ya ki.
Fastoci a Afirka na da mabiya sosai, lokaci zuwa lokaci suna bayyana cewa sun samu albashir daga ubangiji a kan abubuwan da za su faru, wasu lokutta hadda mutuwar manyan mutane.
A shekarar 2016, wani sanannen Fasto dan Najeriya, TB Joshua, ya bayyana cewa ya samu albishir cewa Hillary Clinton za ta kayar da Donald Trump a zaben Amurka.
Mutane sun yi Allah wadai da shi bayan da Trump ya yi nasara. A bayan haka ne aka goge busharar din nasa daga shafin Facebook.