[post by samaila umar lameedo]

Akwai rikici idan APC ta tafka magudi a zaben 2019 - Tsohon gwamnan Niger, Aliyu

- Tsohon gwamnan jihar Nigeria, Babangida Aliyu, ya ce Nigeria zata fuskanci tashin hankali ma damar jam'iyyar APC mai mulki ta tafka magudi a zaben 2019 da ke gabatowa
- Ya ce kan 'yan Nigeria yanzu ya waye saboda yaduwar kafofin sadarwa na zamani, don haka zai yi matukar wahala a gudanar da magudin zabe cikin sauki
- A nashi jawabin, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce in ba don taimakon PDP ba, da jam'iyyar APC ba ta samu nasarar lashe zaben 2015 ba
Tsohon gwamnan jihar Nigeria, Babangida Aliyu, a ranar Alhamis, ya ce Nigeria zata fuskanci tashin hankali ma damar jam'iyyar APC mai mulki ta tafka magudi a zaben 2019 da ke gabatowa. Ya ce 'yan Nigeria da kasashen waje na sa idon don ganin an gudanar da sahihin zabe wanda babu magudi a ciki.
Mr Aliyu ya bayyana hakan a Dutse, jihar Jigawa, jim kadan bayan mika tuta ga wasu 'ya takara a jihar, karkashin jam'iyyar adawa ta PDP.
Ya ce kan 'yan Nigeria yanzu ya waye saboda yaduwar kafofin sadarwa na zamani, don haka zai yi matukar wahala a gudanar da magudin zabe cikin sauki.
Akwai rikici idan APC ta tafka magudi a zaben 2019 - Tsohon gwamnan Niger, Aliyu
Ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari akan zargin da ake yi na cewar iyalansa sun mallaki kaso mai tsoka a bankin Keystone da kuma kamfanin sadarwa na 9Mobile, yana mai cewa "fasahar zamani zata bayyanar da gaskiyar wannan zargi."
Haka zalika, ya ce a lokacin da gwamnatin jam'iyyar PDP take mulki, ta yi kokari fiye da gwamnati mai ci a yanzu ta PDP.
"A duk lokacin da aka samu canjin gwamnati, sabuwar gwamnatin zata rinka cewa gwamnatin da ta shude bata tsinana komai ba, dabarar yin hakan kuwa baya wuce juyar da tunanin jama'a, daga kallon irin rawar da ita gwamnatin mai ci zata taka, da kuma sanya tsanar gwamnatin data shude a zukatan jama'a," a cewar sa. "A cikin shekaru 16 da PDP ta yi a mulki, ta aza harsashen bunkasa tattalin arzikin Nigeria."
A nashi jawabin, a wajen taron, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ce in ba don taimakon PDP ba, da jam'iyyar APC ba ta samu nasarar lashe zaben 2015 ba.
"A 2014, APC tamkar macen da bata iya daukar ciki ce, amma da taimakon PDP, suka samu damar kafa gwamnati," a cewar sa.