Abin hannun da Atiku ya saka ya jawo cece-kuce

Wani bawan Allah ya zargi cewa, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben watan Fabrairu, Atiku Abubakar wai ya saka wani alamar ido a hannunshi da akewa lakabi da Nazar watau wani shu'umin alamar ido da ake samu daga kasar Turkiyya.
Ya kara da cewa, mu gujewa masu siyasar ko a mutu ko a yi rai.
Mu gujewa 'yan siyasa masu shan jini.
Saidai wani masoyin Atiku ma'abocin dandalin Twitter, Gimba Kakanda ya bashi amsar cewa, 'yan Najeriya sai a barsu, abin hannun da Atiku ya saka a bayyane yake amma bana Nazar bane, wanda ake iya samu a shagunan kasar Turkiyya cikin sauki. Ya kara da cewa ni kaina wani malamina ya taba bani shi a matsayin kyautar zagayowar ranar haihuwata.