A Facebook kawai aka san Atiku, Buhari ya fishi, Kyau, tsawo da sanin makamar aiki<>Babachir Lawal

Tsohon sakataren gwamnatin Tarayya, Babachir David Lawal yayi kaca-kaca da dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar inda yace shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fishi komai.
Babachir yayi wannan maganane a hirar da yayi da jaridar The Sun inda ya bayyana cewa, A Facebook kadai aka san Atiku, ya tara yara matasa masu wayau ya rarraba musu na'urar kwamfuta da wayoyin hannu na zamani suna ta babatu da fitar da alkaluman da bana gaskiya ba.
Yace masu zabe na ainihi babu ruwansu da talabijin, ko kuma shiga yanar gizo, yace koda an kawo wuta a garuruwansu basu da lokacin tsayawa su yi kallo, wadannan su idan ka tambayesu wa suka sani Buharine kawai amma PDP suna yaudarar kansu wai sune a gaba.
Ya kara da cewa, Buhari yawa Atiki fintinkau a fannin gaskiya, yafi Atiku Tsawo, yafi Atiku kyau, yafi Atiku sanin makamar aiki saboda shi ya zama shugaban kasa, Atiku kuwa mataimakin shugaban kasa kadai ya taba rikewa.
Ya kara da cewa dan haka ko ta ina Buhari yafi Atiku.