Online counter

Shugabanin kabilar Yarabawa sun goyi bayan Atiku

[post by samaila umar lameedo]

Shugabanin kabilar Yarabawa sun goyi bayan Atiku

Wasu fittatun shugabanin Yarabawa karkashin kungiyar South-West Forum sun goyi bayan dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar a zaben shekarar 2019.
A karshen taron da suka gudanar mai taken '2019: South-West Speaks', shugabanin Yarabawan sun yanke shawarar goyon bayan Atiku ne saboda alkawarin da ya yi na sauya tsarin rabon arziki na kasa idan an zabe shi.
An gudanar da taron ne a Muson Centre da ke Onikan a jihar Legas.
Wani fittacen jagoran Yarabawa, Dr. Remi Akitoye ne ya gabatar da kudirin zaban Atiku a matsayin dan takarar da yankin Kudu maso yamma za ta zaba a zaben 2019, sannan dukkan sauran mahalarta taron suka amince da hakan.
A yayin da ya karanto sakon bayan taron, Prince Uthman Shodipe ya bayyana cewa yankin Kudu maso yamma ta cimma matsaya na goyon bayan Atiku a zaben sh
Ya ce shugabanin Yarabawa za su cigaba da kasance tsintsiya madaurinki daya kuma sunyi imani da cewa yiwa tsaron rabon arzikin kasa garambawul shine abinda zai kawo masala a kasar.
Uban taron, Farfesa Banji Akintoye ya ce al'ummar Yarabawa ba su taba shiga cikin matsanancin talauci kamar yanzu ba, "irin talaucin da ba mu taba gani ba".
Amma ya yi imanin cewa al'ummar Yarabawan za su mike tsaye domin yaki da talaucin da ya yi musu katutu.
Wadanda suka hallarci taron sun hada da dan takarar gwamnan PDP na jihar Legas, Mr Jimi Agbaje da abokiyar takararsa, Mrs Haleemat Busari, dan takarar gwamnan na Advanced Democratic Party (ADP), Babatunde Gbadamosi da PDP dan takarar gwamnan PDP na jihar Oyo, Engr. Seyi Makinde da sauran jiga-jigan jam'iyyun siyasa da shugabanin yarabawa.

Post a Comment

0 Comments