[post by samaila umar lameedo]

Sanata Ahmed Aruwa ya rasu

LABARAI DAGA 24BLOG
Allah Ya yi wa Sanata Ahmed Aruwa rasuwa tsohon dan majalisa tarayya daga jihar Kaduna.
Aruwa wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa tsakanin 1999 zuwa 2003, ya rasu ne bayan doguwar jinya.
Daya daga cikin yaransa na siyasa Abdullahi Akilu Jugnu wanda ya tabbatar wa da BBC da labarin rasuwarsa, ya ce da misalin karfe 4 na dare ne Allah ya karbi ransa.
Kuma ya ce ya rasu ne a wani asibiti da ke unguwar Barnawa a Kaduna.
Da misalin karfe daya na rana ne za a yi jana'izarsa a masallacin Sultan Bello a Kaduna.
'Yadda masu yada labaran karya suka kashe ni'
Gaskiyar abin da na fada kan zaben Buhari - IBB
Sanata Aruwa wanda ya taba tsayawa takarar gwamnan Kaduna a 2007 karkashin jam'iyyar ANPP ya rasu ya bar 'ya'ya takwas a duniya, mata shida da maza biyu.
Jugnu ya ce 'ya'yansu uku mata da namiji daya dukkaninsu suna tare mahaifiyarsu a kasar Amurka. Kuma daya daga cikin 'ya'yansa tana aiki ne da hukumar bincike ta FBI.