[post by samaila umar lameedo]

Modric ya lashe kyautar Ballon d'Or ta 2018

LABARAI DAGA 24BLOG
Dan wasan Croatia da Real Madrid, Luca Modric ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na 2018, wato Ballon d'Or ta 2018.
Modric shi ne ya lashe kyautar dan wasan da babu kamarsa a gasar cin kofin duniya da aka yi a Rasha a 2018, wadda Faransa ta lashe.
Haka kuma shi ne wanda aka zaba a matakin dan kwallon da ya fi yin fice a nahiyar Turai a shekarar nan.
Dan kwallon Portugal da Juventus, Cristiano Ronaldo ne zakaran 2017, kuma yana cikin 'yan takara har da Lionel Messi na Barcelona
'Yar wasan tawagar kwallon kafar Norway, Ada Hegerberg ce ta lashe kyautar Ballon d'Or ta mata a karon farko da aka sa mata a cikin bikin karramawar.
'Yar wasan mai taka leda a Lyon mai shekara 23, ta ci kofin Zakarun Turai uku da na gasar kwallon Faransa hudu da na kalubalen Faransa.