[post by samaila umar lameedo]

Kasaer da aka martaba dabbobi fiye da tsoffin shugabanni

LABARAI DAGA 24BLOG
Gwamnatin Kenya ta sauya hotunan tsoffin shugabannin kasar da ke jikin kudinta zuwa hotunan namun daji.
Wasu na ganin hakan wani kokari ne na dakushe ayyukan ci gaba da suka yi wa al'umarsu.
An maye gurbin hotunansu da na dabbobi a jikin sabbin kudin sulallan Kenya wanda a baya ya kunshi hotunan shugabanni uku da suka yi rawar gani a kasar cikinsu har da shugaban farko Jomo Kenyatta.
An samu banbancin ra'ayi tsakanin al'umar Kenya, wasu na ganin matakin wani yunkuri ne na shafe bajintar tsofaffin shugabannin, yayin da wadansu ke ganin, gwamnatin na son amafani da hakan don neman suna.
Wasu kuma na kallon hakan a matsayin rashin girmama mutanen da suka taka muhimmiyar rawa a jagorancin al'umma.
'Ba laifi ba ne' yin jima'i a mota a Najeriya
Tsawa ta hallaka mutum 10
A baya sabbin sulallan dai na dauke da hotunan shugabanni uku na kasar wato Daniel Arao Moi da Mwai Kibaki sai kuma mahaifin shugaba mai ci Jomo Kenyatta.
A yanzu hotunan manyan namun dajin kasar ne aka sa aka a kudin da suka hada da Karkanda da Zakuna da Giwaye da kuma Rakumin dawa.
Duk da cewa Shugaba Uhuru Kenyatta Da ne ga shugaban kasar na farko da aka sauya hotonsa ya ce wannan gagarumin sauyi ne mai matukar muhimmanci ga 'yan kasar.
Kowanne daga cikin tsofaffin shugabannin an buga hotonsa a jikin sulallan a lokacin da ya yi mulki.
Shugaba Kibaki ya yi nasarar zama shugaban Kenya a shekarar 2002 abin da ya kawo karshen mulkin shugaba Moi da ya dauki shekara 24 a kai.
Kibaki ya yi alkawarin ba zai sanya hotonsa a jikin kudin kasar ba amma kuma ya karya wannan alkawarin.
Tashin hankalin da ya biyo bayan hakan shi ya sanya aka matsa lambar sauya kudin tsarin mulki da aka fara amfani da shi karkashin tsarin dimukradiyya a shekara ta 2010, dokar ta tanadi babu waani shugaba ko wani dan kasar nan gaba da za a kara sanya hoton shi a jikin kudin kasar.
A yanzu dai babban bankin Kenya ya fara amfani da dokar akan sulallan. Inda hoton zaki ne aka saka a shillin 10, sai Giwa a shillin 20, sai Karkanda ashillin 5 da Rakumin dawa a jikin shillin 1.
Watakila nan gaba a sauya takardun kasar da har yanzu Shillin 1000 ke dauke da hoton mahaifin shugaba Uhuru Kenyattta kuma tsohon shugaban Kenya Jomo Kenyatta.
Labarai mas