[post by samaila umar lameedo]

Gaskiyar abin da na fada game da sake zaben Buhari - IBB

LABARAI DAGA 24BLOG
Tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya gasgata wasikar da aka ce ya rubuta game da adawa da sake zaben Buhari a wa'adi na biyu.
A watan Fabrairu ne aka wallafa wata wasika da aka ce ta fito ne daga tsohon shugaban inda a ciki ya bukaci shugaba Buhari ya janye neman wa'adin shugabanci na biyu, ya ba matasa dama.
Daga baya IBB ya musanta cewa shi ya rubuta wasikar, amma a wata hira da aka yi da shi da jaridar Premium Times ta wallafa ranar Lahadi, tsohon shugaban ya amsa daukar alhakin rubuta wasikar.
IBB ya ce 'yan jarida ne suka sauya asalin abin da ya fada a cikin wasikar bayan an tambaye shi dalilin da ya sa ya musunta bayan fitar da wasikar.
Tsohon shugaban ya ce 'yan jarida ya zarga, domin abun farko da wani ya ce, "IBB ya ce Buhari ya yi tsufa da zama shugaban kasa, ko wasu kanun labaran da ba su dace ba da za su gama ni fada da shugaban kasa. Ba ni son shiga fada kan abin da ban ce ba."
Me ya sa Atiku ya ce jam’iyyar APC na sayen katin zabe?
Buhari 'na son yin watsi da kudirin dokar zabe'
Mai magana da yawun tsohon shugaban ne Kassim Afegbu ya fitar da wasikar, kuma a ciki ya yi kira ga shugaba Muhammadu Buhari da kada ya tsaya takara a 2019.
Amma daga baya IBB ya ce, "Bayanan da aka fitar a cikin wasikar da aka danganta da ni ba nawa ba ne."
Tsohon shugaban ya ce, "Babu wani shinge tsakani na da masu rike da madafan iko a Najeriya."
Kafin dai IBB ya fitar da wasikar game da sake zaben Buhari, tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo da Janar Theophilus Danjuma sun rubuta wasikar nuna adawa da gwamnatin Buhari.
An tambayi IBB, hakan ko yana nufin dukkaninsu tsoffin shugabannin na soja sun hade wa Buhari kai ne kafin zaben 2019? Sai IBB ya ce 'yan jarida ne kawai suka kirkiri haka.
Ya ce bayan Janar Obasanjo da Janar Danjuma sun rubuta wasikarsu, kafin ya rubuta ta shi, kawai sai 'yan jarida suka yanke hukunci cewa sun hade wa Buhari kai ne. "Babu wani hade kai, kawai tunanin 'yan jarida ne," in ji IBB.