[post by samaila umar lameedo]
Buhari yayi tir da rikicin Kuros Ribas

LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaba Muhamadu Buhari ya nuna damuwarsa dangane da rikicin da ya barke tsakanin wasu al'umomi hudu a karamar hukumar Biase ta jihar Kuros Ribas.
Rikicin ya janyo rasa rayuka da rauni ga wadanda abin ya rutsa da su, inda har wasu mazauna kauyukan yankin suka gudu suka bar muhallansu.
Shugaban ya nemi masu rikicin da su sasanta tsakaninsu a wannan yankin da ke makwabtaka da jihar Abiya.
"Ya kamata al'umomin su zama cikin shirin sasantawa da zaman lumana tun da ba za a sami ci gaba ba idan babu kwanciyar hankali," inji shugaban.
Abun da zai faru a Najeriya da makwabta a wannan makon
Buhari ya mayar wa Nnamdi Kanu martani
Ya kuma yaba wa gwamnatin jihar saboda matakan da ta dauka da suka dakile bazuwar lamarin.
Ya kuma jinjina wa rundunar 'yan sanda da ke jihar saboda yadda suka tura jami'ansu cikin gaggawa zuwa wuraren da rikicin ya auku domin kawo karshen rikicin.