Online counter

An rage farashin mai a Faransa saboda zanga-zanga

[post by samaila umar lameedo]

An rage farashin mai a Faransa saboda zanga-zanga

LABARAI DAGA 24BLOG
Firaministan Faransa Edouard Philippe ya bayyana cewa dole ne gwamnati ta saurari koken jama'a sannan matakin da aka dauka na kara haraji a kasar na bukatar tattaunawa cikin tsanaki kafin cimma matsaya.
An shafe mako uku ana gudanar da zanga-zangar a manyan biranen Faransa, al'amarin da ya jawo lalacewar abubuwa da dama.
Masu zanga-zangar da ke sanye cikin shudayen ruguna da ake ma lakabi da 'gilets jaune' na ci gaba da karuwa ta hanyar kwarmata zanga-zangar a shafukan sada zumunta da kuma nuna fushinsu ga gwamnatin kasar.
Mutum uku ne suka mutu tun farkon fara zanga-zangar wacce ta jawo tashin hankali da lalata abubuwa - musamman da aka rusa wasu mutum-mutumi a Arc de Triomphe da ke Paris a ranar Asabar din da ta gabata.
Hukumomin kasar sun yi Allah wadai al'amarin
Zanga-zangar ta biyo bayan matakin da gwamnatin shugaba Emmanuel Macron ta dauka na kara harajin mai a kasar.
Farashin man dizel a kasar ya samu karuwa da kashi 23 cikin a cikin watanni 12 da suka gabata, kari mafi girma cikin shekaru 18.
Farashin mai a kasuwar duniya dai ya samu karuwa cikin watannin da suka gabata kafin ya kuma faduwa cikin makonnin da suka wuce.
Amma duk da hakan gwamnatin shugaba Macron ta kara harajin mai a kasar da centi 7.6 kan kowacce litar man dizel da kuma centi 3.9 kan kowacce litar man fetur.
Shekara biyu da suka shude ne dai aka zabi Shugaba Emmanuel Macron bisa doron tarun alkawuran kawo sauyi kan tattalin arzikin kasar, sai dai farin jinin shugaban na ci gaba da raguwa cikin watannin baya-bayan nan bisa irin abubuwan da ke gudana karkashin jagorancinsa.
Shugaba Macron dai ya soki 'yan adawar kasar da iza wutar zanga-zangar domin shafa masa kashin kaji.

Post a comment

0 Comments