[post by samaila umar lameedo]

Zuwan su Buratai kaddamar da kamfen din Buhari: Garba Shehu ya yi karin haske

LABARAI DAGA 24BLOG
A jiya, Litinin, ne jaridar Punch ta wallafa wani rahoto da jam'iyyar PDP ke korafin ganin shugabannin rundunar soji da na hukumomin tsaro a wurin kaddamar da yakin neman zaben Buhari.
A cikin rahoton, PDP ta bukaci fadar shugaban kasa ta yi bayanin dalilin ganin shugabannin hukumomin tsaro da na rundunar soji a wurin taron siyasa bayan doka ta haramta ma su shiga harkar siyasa ta kowacce fuska.
Sai dai kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, ya ce bai ma kamata a ke korafi a kan zuwan su Buratai wurin ba, domin sun je ne bisa kuskuren cewar taron ba na siyasa ba ne.
Garba Shehu
"Kamata ya yi jaridar Punch ta tamabayi mai ya kai shugabannin hukumomin tsaro da na rundunar soji wurin taron "Next level 2019" a fadar shugaban kasa, amma su ka ta fi kafin a fara gabatar da komai.
DUBA WANNAN: Sojojin Najeriya kadai ba zasu iya gamawa da Boko Haram ba - Buhari
"Sun zo ne domin yin bayani a kan nasarorin da hukumomin da su ke jagoranta su ka samu, bisa kuskuren tunanin cewar taron ba na siyasa ba ne.
"Da zuwansu ko zama ba su yi ba sai ministan tsaro, Birgideya Janar Mansur Dan-Ali (mai ritaya) ya ce bar wurin taron domin na siyasa ne, kuma nan da nan su ka tafi tun kafin ma shugaban kasa ya fito," a cewar Garba Shehu.