[post by samaila umar lameedo]
Yadda hayaniya ke tasiri ga marassa lafiya a asibitoci

LABARAI DAGA 24BLOG
Masu bincike sun gano cewa, ana samun karuwar hayaniya ko kara marar tushe a asibitocin duniya.
Masu binciken sun ce duk mutumin da zai shafe dare a asibiti, to zai dandana kudarsa domin kuwa bacci sai dai barawo, saboda karar abubuwa da dama ta kan hana mutum sukuni.
Masu binciken sun ce hayaniya kamar ta ma'aikatan asibitin da injina da kuma ta wayoyin salular mutane ko ta asibitin, ko ma ta mutanen da ke jinyar marassa lafiya kadai sun ishi mutum ya kasa bacci.
Gurbatar yanayi - Hanyoyi biyar na inganta tsaftar iskar cikin gida
Rashin lafiyar tabin hankali na karuwa a duniya
Hanyoyin da za a kauce wa kamuwa da ciwon suga
Binciken ya gano cewa, a Birtaniya, kaso 40 cikin 100 na marassa lafiyar da ke kwance a asibiti na matukar damuwa da irin hayaniya ko karar d ake damunsu a cikin dare.
Masu binciken suka ce ba wai marassa lafiya ko masu jinya ne kadai wannan hayaniya ke damu ba, hatta su kansu ma'aikatan da ke asibitin wannan hayaniya na shafar aikinsu da ma kwazonsu.
Masu binciken wadanda suka fito daga King's College da ke Landan, sun ce yanzu hayaniya ko karar ta kan damu marassa lafiyar da ke kwance a dakuna bayar da kulawa na musamman wato ICU.
Masu binciken suka ce saboda irin wannan hayaniya ko karar, kan sa mafi yawancin marassa lafiya barin asibiti ba tare da sun warke ba, saboda su samu saukin hayaniya ko sa samu su murmure da wuri.
Daga karshe masu binciken, sun yi kira ga gwamnatocin kasashe da ma masu ruwa da tsaki da a hada kai wajen lalubo hanyar magance ko kuma rage hayaniya da kara marar dalili a asibitoci.