[post by samaila umar lameedo]
Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi Faransa

LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tafi birnin Paris na kasar Faransa don halartar wani babban taro kan zaman lafiya.
Za a gudanar da taron ne tsakanin ranakun Lahadi zuwa Talata masu zuwa, amma ya bar Abuja ne a ranar Juma'a.
Mai taimaka wa shugaban kasar kan harkar yada labarai Femi Adesina ya ce gwamnatin kasar Faransa da wadansu kungiyoyi masu zaman kansu ne suka shirya.
Ya kuma ce an shirya taron ne "don magance manyan kalubalen duniya da kuma samar da tabbataccen zaman lafiya."
Hotunan yadda Aisha Buhari ta karrama 'yan fim
Masu dogon baccin safe sun fi kamuwa da sankara
Karin albashi: 'Yan fansho na son a tuna da su
Shugaban tare da Babban Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres da sauran shugabannin kasashen duniya ne za su halarci taron.
Hakazalika shugaban tare da sauran shugabanni za su halarci taron tunawa da yarjejeniyar Armistice wadda ta kawo karshe yakin duniya na farko.
Har ila yau shugaban zai gana da 'yan Najeriya mazauna kasar Faransa.