Shugaba Buhari yace kowa ya zabi wanda yake so

LABARAI DAGA 24BLOG
Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yanzu kam 'yan Najeriya tuni suka waye domin kuwa lokacin murdiyar zabe, satar akwati da kuma anfani da hukumomin gwamnati don yin magudin zabe dukkan su sun wuce.
Haka zalika shugaban kasar ya kara da cewa yana shawartar 'yan Najeriya a ko'ina suke da su darje su zabi wanda ran su ke so a zabukan gama gari na shekarar 2019 masu zuwa a dukkan matakai.
Ba sauran sak: Shugaba Buhari yace kowa ya zabi wanda yake so
Shugaban kasar yayi wadannan kalaman ne lokacin da ya karbi bakincin wasu manyan jami'an majalisar dinkin duniya da kuma shugabannin kungiyar kasashen yammacin Afrika a ofishin sa dake Abuja.
Haka zalika shugaban kasar ya kuma bayar da tabbacin cewa gwamnatin sa zata yi dukkan iya kokarin ta wajen ganin zabukan na 2019 sun kasance sahihai a kowane irin ma'auni.