Satar dukiyar jama'a: Kungiyar CUPS za ta cirewa Gwamna Abdulaziz Yari zani a kasuwa

LABARAI DAGA 24BLOG
[Post by samaila umar lameedo]
Mun samu labari cewa kashin Gwamna Abdulaziz Yari na Jihar Zamfara ya bushe bayan an fara binciko wasu asiran sa. Yanzu haka Yari ne Shugaban Kungiyar nan ta NGF na Gwamnonin Jihohin Najeriya kaf.
Yari yana amfani da wani asusun UBA wajen sace kudin Zamfara
Wata Kungiya da tayi fice wajen bankado badakaloli da tona asirin masu laifin Najeriya mai suna CUPS ta sanar da cewa wasu takardu da za su tona asirin Gwamna Abdulaziz Yari sun shigo hannun ta kuma za ta fallasa sa nan gaba kadan.
Kungiyar ta CUPS da ke Kasar Birtaniyya ta bayyana cewa tana da wasu takardu da ke nuna yadda Gwamna Abdulaziz Yari ya rika satar kudi daga asusun Jihar Zamfara na tsawon shekaru kusan fiye da 7 da yayi yana mulkin Jihar.
Shugaban wannan Kungiyar ta CUPS watauDr. Idris Ahmed ya bayyana wannan ne a shafin sa na sadarwa na zamani. Ahmed yace nan ba da dadewa ba zai taso Gwamnan a gaba ya nunawa Duniya irin ta’asar da yayi da Baitul Malin Jihar sa.
Dr. Idris Ahmed ya bayyana cewa Gwamnan ya hada kai ne da Kwamishinan sa na kudi wajen yin wannan aika-aika na tsawon shekarun da yayi yana mulkin Jihar. Yari ya zama Gwamna ne a 2011 inda yanzu yake sa ran tafiya Majalisar Dattawa.
Yanzu haka dai Gwamna Yari yana kokarin ganin wannan Kwamishina na sa na kudi watau Alhaji Mukhtar Shehu Idris ya samu tikitin takarar kujerar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki a 2019.