Saboda a zauna lafiya a Kano na fasa takarar Shugaban kasa na koma APC – Malam Shekarau

LABARAI DAGA 24BLOG
Mun samu labari cewa Ibrahim Shekarau wanda ya taba yin Gwamna a Jihar Kano daga 2003 zuwa 2011 yayi hira da Jaridar Daily Trust kwanaki inda yayi magana game da yadda zaben badi zai kasance.
Mal. Shekarau ya fice daga PDP ya bi Ganduje a Jam’iyyar APC
Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa an dauki Jam’iyyar PDP an mikawa Rabiu Musa Kwankwaso bayan ya sauya-sheka zuwa PDP. Shekarau yace wannan zalunci yana cikin abin da ya sa ya fice daga Jam’iyyar PDP ya dawo APC.
Tsohon Gwamnan yace ya hakura da takarar kujerar Shugaban kasa a PDP ne har ta kai ya fice daga Jam’iyyar domin ayi sulhu a zauna lafiya a Jihar sa ta Kano. Yanzu dai Malam Shekarau zai nemi kujerar Sanatan Kano a APC.
Kwankwasiyya za su yi nadama a 2019 domin kuwa yanzu manyan kusoshin PDP sun fara barin Jam’iyyar adawar su na komawa PRP.
Ibrahim Shekarau ya kuma bayyanawa manema labarai cewa wasu Jiga-jigan PDP sun ajiye harkar siyasa a yanzu bayan zuwan ‘Yan Kwankwasiyya don haka babu wadanda aka bari a PDP sai Magoya-bayan Magajin na sa Sanata Kwankwaso.
Yanzu haka dai za a gwabza da Ibrahim Shekarau a zaben 2019 wajen karbe kujerar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Malam Shekarau dai yace ko da wa zai yi takarar kujerar na Kano ta tsakiya ba ya jin tsoro domin kuwa ya shiryawa zaben tsaf