[post by samaila umar lameedo]
Sojojin Najeriya 'sun kashe' kwamandojin Boko Haram

LABARAI DAGA 24BLOG
Rundunar sojin Najeriya ta yi ikirarin cewa dakarunta sun kashe kwamandojin kungiyar Boko Haram a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.
Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter da safiyar ranar Lahadi ta kara da cewa dakarunta sun kwace wasu kauyuka daga hannun mayakan kungiyar.
"An kashe Abu Rajal da Tuja Sa'inna Banki ne lokacin da ake kakkabe yankunan (Gumsuri da Gambori) daga 'yan Boko Haram. Babban hafsan rundunar sojin kasa Laftanar Janar TY Buratai ya yaba wa dakarun da suka yi wannan aiki sannan ya bukace su da su ci gaba da kakkabe ragowar mayakan Boko Haram," in ji sanarwar.
Rundunar sojin ta yi wannan karin haske ne a daidai lokacin da mayakan Boko Haram suka kai hari a kauyuka biyu da ke kusa da garin Maiduguri ranar Asabar da almuru.
Shigar IS rikicin Boko Haram ta kara dagula lamura ne?
Boko Haram ta kai hari kusa da Maiduguri
Ina 'yan sanda suka ajiye 'yan Shi'a 400 da suka kama?
Harin — wanda ake ganin wani yunkuri ne na kokarin shiga Maiduguri —ya tilasta wa mazauna kauyukan tserewa daga gidajensu.
Rahotanni sun ce an kai harin ne a unguwar Polo da ke wajen Maiduguri da kuma kauyukan Bale Shuwari da Jimine da ke bayan Giwa Barracks inda kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare.
Mazauna yankin sun ce an shafe lokaci suna jin karar harbe-harbe da tashin bama-bamai.