PDP ta yi watsi da Olujimi ta tabbatar da jagorancin Fayose a Ekiti

LABARAI DAGA 24BLOG
[post by samaila umar lameedo]
Mun samu labari daga Jaridar Punch cewa Jam’iyyar PDP a Jihar Ekiti ta tabbatar da mubaya’ar ta ga tsohon Gwamnan Jihar watau Ayodele Fayose bayan a da an tunbuke sa daga matsayin na sa.
Shugannin PDP sun ce su na bayan Fayose har gobe a Jihar Ekiti
Manyan PDP a Jihar Ekiti sun musanya cewa sun tsige Ayo Fayose daga mukamin sa na Jagoran Jam’iyya a Jihar tare da nada Sanata Biodun Olujimi a matsayin wanda za ta maye gurbin tsohon Gwamnan a babbar Jam’iyyar adawar.
Shugabannin PDP na Ekiti sun jaddada goyon bayan su ga Mista Ayo Fayose wanda ya bar kujerar Gwamnan kwanan nan. Shugabannin Jam’iyyar da su ka dauki wannan mataki sun hada har da Jagororin PDP na Kananan Hukumomi.
Sauran kusoshin Majalisar ta SEC da su ka dauki wannan mataki akasin abin da mu ka ji labari kwanaki sun hada da Sakatororin Jam’iyya a fadin Jihar da kuma sauran masu rike da mukamai dabam-dabam a PDP da Jiga-jigan Jam’iyya a fadin Jihar.
A taron da PDP ta shirya, an fitar da jawabi cewa tsohon Sakataren Jam’iyyar na Jihar watau Dr. Tope Aluko da kuma Sanata Biodun Olujimi su na yi wa APC aiki ne da rigar PDP a boye. Jam’iyyar ta ce su Aluko na kokarin ganin bayan PDP ne.
A jiyan dai Shugaban Jam’iyyar PDP na Ekiti Gboyega Oguntuase ya bayyanawa jama’a cewa su na tare da Atiku Abubakar a aben 2019 sannan kuma yace mubaya’ar su tana wajen tsohon Gwamnan Jihar Ayodele Fayose ba Biodun Olujimi ba.
A baya kun ji cewa an soke dakatarwar da aka yi wa Dr. Tope Aluko daga Jamiyyar. Sai dai Shugaban PDP na Jihar ya nuna cewa bai ji dadi da aka yi masa afuwa domin ana zargin sa da kitsa rikici a PDP.