[post by samaila umar lameedo]
Najeriya ta bai wa Amurka shawara kan Atiku Abubakar

LABARAI DAGA 24BLOG
Gwamnatin Nigeria ta bai wa Amurka shawara kan cewa ya kamata ta yi cikakken bayani idan har ta amince za ta bai wa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar izinin shiga kasar.
Gwamnatin ta nuna damuwa dangane da yunkurin neman bai wa tsohon mataimakin shugaban izinin shiga Amurka, wanda a baya aka hana shi, tana mai cewa yin hakan tamkar Amurkar tana nuna goyon baya ne ga takararsa.
Ministan watsa labarai da al'adu na Najerya Alhaji Lai Mohammed, ya ce gwamnati ba ta son a kai wani yanayi da zai nuna tamkar an fifita wani dan takara a kan wani.
Wasu kafofin watsa labarai na kasar sun nuna cewa gwamnatin Amurka na shirin bai wa dan takarar shugaban Najeriya a jam'iyyar PDP Atiku Abubakar takardar izinin shiga kasar.
To sai dai gwammnatin ta Amurka ba ta ce komai ba dangane da batun ba.
Zaben Najeriya: An soma fafatawa tsakanin Atiku da Buhari
Wanne dan takara Rahama Sadau za ta zaba tsakanin Atiku da Buhari?
Buhari da Atiku: Amurka da EU na son a rungumi zaman lafiya
Lai Muhammad ya ce Amurka a matsayinta na kasa, tana da 'yanci ta bai wa kowane mutum takardar iznin shiga kasarta.
"Amma idan aka yi la'akari da matsalolin da Atiku ya ci karo da su shekaru 10 da suka gabata wajen samun takardar Visa, ya kamata Amurka ta yi taka tsan-tsan kada a fassara yunkurin ba shi Visar da cewa Amurkar tana goyon bayan takararsa," a cewar Lai.
Ya ce kamata idan yanzu Amurka ta yanke hukuncin za ta ba shi takardar izinin shiga, to ya kamata su yi bayani ko me ya sauya, saboda ya zama dan takarar babbar jam'iyyar adawa ne yasa aka ba shi?
"Ya kamata su fito su yi bayanin ko me ya canza."
BBC ta tambayi Lai cewa a baya Atikun ya shaida wa BBC cewa ofishin jakadancin Amurka sun ce masa ana nazari a kan takardarsa ta neman viza, ba ya ganin cewa mai yiwuwa sai yanzu Amurkar ta gamsu da bukatar neman shiga kasar da ya yi shi yasa take tunanin ta ba shi a halin yanzu?
Sai Lai ya ce, "A'a, ai gwamnatin Amurka ce ta fara bincike har aka samu wani dan Majalisa da laifin cin hanci da rashawa, kuma idan aka tuna a shekarar 2006 hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta Amurka ta kai sumame gidan wani dan Majalisar, har ta samu makuden kudade a na'urar sanyaya abinci, kuma a kan zargin cewa shi Atikun yana da hannu wajen neman karbar hanci.
"Amma mu ba abin da muke magana a kai ba ne yanzu, mu abin da muke cewa shi ne idan a shekarun baya ba a ga ya cancanta ba, yin haka yanzu zai aike da wani sako da bai da ce ba.
A baya dai tsohon mataimakin shugaban kasar ya shaida wa BBC cewa ba dole ne shiga Amurka ba. Sannan ya musanta cewa ya yi gwanjon gidansa da ke Amurka saboda batun zargin rashawa.
Masu hamayya da Atiku dai na yi masa kallon wanda ya ke da tabon cin hanci da rashawa, to sai dai dan takarar na PDP ya kalubalanci duk masu zarginsa da su kawo kwarararn hujjoji.