Mutum 50 aka kashe a rikicin 'yan Shia a Abuja —Burtaniya

LABARAI DAGA 24BLOG
Burtaniya ta ce mutum 50 aka kashe a arangamar da aka yi tsakanin 'yan Shia da jami'an tsaron Najeriya a Abuja a makon jiya
Kungiyar 'yan Uwa Musulmi ta 'yan Shia mabiya Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ta ce an kashe mambobinta fiye da 50, ko da yake rundunar sojin kasar ta ce mutum uku ne suka mutu a rikicin.
Sanarwar da wata mai magana da yawun ofishin jakadancin Burtaniya a Najeriya, Louise Edwards ta aike wa manema labarai ranar Lahadi, ta ce kasarta ta bayyana wa gwamnatin tarayyar Najeriya matukar damuwa kan rikicin da kuma yawan mutanen da aka kashe sakamakonsa.
Sanarwar ta bukaci bukaci dakarun tsaron Najeriya su rika gudanar da ayyukansu bisa dokokin kasashen duniya da na cikin gida da kuma kare hakkin farar hula.
Mun kashe 'yan Shi'a a Abuja — Sojin Nigeria
Yadda za a sasanta tsakanin gwamnati da 'yan Shi'a
Ofishin jakadancin na Burtaniya ya yi maraba da alkawarin da gwamnatin Najeriya ta yi na gudanar da cikakken bincike kan batun da kuma alwashin da ta sha na hukunta duk jami'in tsaron da ya keta doka lokacin rikicin.
Rikicin ya fara ne a lokacin da 'yan Shi'a suka fara tattakin Arbaeen na shekara-shekara a Abuja - wato tarukan tunawa da kisan jikan Manzon Allah (SAW).
'Ba sa dauke da makamai'
A lokacin tattakin, 'yan Shi'a sun neman saki jagoransu Sheikh Ibrahim El-Zakzaky wanda ake tsare da shi kimanin shekara uku da suka wuce, bayan wani rikici da kungiyar ta yi da sojoji a Zaria.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta soki gwamnatin Najeriya kan kisan 'yan Shia, tana mai cewa kisan "mutanen da ba sa dauke da makamai take hakkin dan adam ne."
Daga bisani rundunar sojin Najeriya ta wallafa wani bidiyon na Shugaban Amurka Donald Trump wanda ta kafa hujja da shi wuri bude wa 'yan Shi'a wuta.
A cikin bidiyon, Shugaba Trump ya ce sojoji za su iya amfani da karfi kan baki 'yan ci rani da ke jifansu da duwatsu.
"Idan suka yi jifa da duwatsu... ku dauka sun yi da bindiga ne," in ji Mista Trump a wani faifan bidiyo.
Rundunar sojin ta goge bidiyon bayan ta sha suka daga wurin 'yan kasar.