[post by samaila umar lameedo]
Mourinho ya kalubalanci ma su sukarsa kan Rashford

LABARAI DAGA 24BLOG
Jose Mourinho ya mayar da martani ga masu sukarsa kan yadda ya nuna bacin ransa bayan Marcos Rashford ya barar da wata dama a wasan da Manchester United ta doke Young Boys da ci 1-0.
Manchester ta tsallake zuwa mataki na gaba da maki 10 bayan Juventus ta doke Valencia.
Rashford ya yi gaba da gaba da gola, amma ya harba kwallon saman raga, abin da ya fusata Mourinho ya juya yana girgiza kai.
Sannan Mourinho ya ja hankali kan yadda ya yi watsi da kwalaben ruwa lokacin da Marouane Fellaini ya jefa wa Manchester United kwallo a ragar Young Boys ana dab da tashi wasa.
Mourinho ya ce ya shiga damuwa kafin lokacin, amma ya samu sauki bayan zura kwallon a raga.
Sai dai wasu na ganin abin da Mourinho ya yi bai dace ba.
Kuma Gary Lineker na daya daga cikin wadanda suka soki Mourinhon.
Lineker ya ce idan ya ga koci irin haka, shi zai tabbatar da cewa yana da tsauri.
Amma Mourinho ya mayar da martani yana cewa zai so ma su sukarsa su karbi aikinsa na horar da 'yan wasa.
Ya ce ba duk koci ba ne zai iya hakuri da wani abin takaicin da ya gani ba.
Mourinho ya ce yana tunanin duk wani kwarararen manaja ba zai iya sukar dan uwansa ba.
Hotunan Mourinho