[post by samaila umar lameedo]
Me yasa OakTV ke baiwa Ministan sadarwa hakuri kan tonon ko nawa wai ake kashewa El-Zakzaki?

LABARAI DAGA 24BLOG
- Gidan talabijin na Oak ya nemi afuwar want minista
- Gwamnati tana kashe N 3.5m wajen ciyar da Alzakzakiy a wata
- Muna neman afuwa sannan munyi nadamar wannan abu
Me yasa OakTV ke baiwa Ministan sadarwa hakuri kan tonon ko nawa wai ake kashewa El-Zakzaki?
Gidan talabijin na OAK ya nemi afuwar ministan watsa labarai Lai Muhammed a bisa wani bidiyo daya watsa inda ministan ya bayyana cewa gwamnati tana kashe makudan kudade wajen ciyar da Alzakzakiy wanda yake daure tun a shekara ta 2015.
Amma abin mamaki a ranar Alhamis wannan bidiyo ya fara yawo a kafafen sadarwa.
A wasikar ban hakuri da gidan talabijin din ya turawa ministan sunce*" A ranar Laraba 7 ga Nuwamba 2018 gidan talabijin dinmu ya samu tangarda a bangaren hira da muka gudanar da ministan watsa labarai ".
Muna neman afuwa da kuma yafiya a bisa wannan kuskure.
Bidiyon yana dauke da ministan ne a lokacin da yake wasu bayanai akan Alzakzakiy.
Inda yake cewa "Anata neman inda zakzakiy yake to yana nan kuma ana ci dashi."
"Gwamnati tana kashe N3.5m a wajen ci dashi a wata".
Inda Ministan tafiye tafiye Rotimi Amaechi ya katse shi ta hanyar ce masa "in kuwa haka ne shima zaizo su kamashi".